13 Mayu 2020 - 06:20
Iran : Za’a Bude Masallatai Domin Raya Darairen Lailatul Kadari

A nan Iran yau Talata ake sake bude masallatai a fadin kasar domin gudanar da ibada a cikin darairen lailatul Kadari.

(ABNA24.com) A nan Iran yau Talata ake sake bude masallatai a fadin kasar domin gudanar da ibada a cikin darairen lailatul Kadari.

Za’a bude masallatan ne da aka rufe a matakan yaki da annobar Korona na tsawon kwanaki uku masu daraja dake tunkarowa na watan Ramadana mai alfarma cewa da lailatul kadari, kamar yadda kwamitin yaki da cutar corona a kasar ya sanar.

Saidai za’a gududanar da ibadar ne kawai na tsawan sa’o’I biyu, kuma a cikin filin masallaci idan son samu ne, a masallatan da basu da fili kuwa za’a yi amfani da kashi guda cikin hudu na cikin masallacin.

Za’a kuma tabbatar mutane sun sanya takunkumi da safar hannu da kuma sanya tazara tsakaninsu yayin gudanar da ibadun.

An kuma bukaci jama’a su zo da abubuwan gudanar da ibadarsu irinsu litaffen adu’o’I da al’kurani mai tsarki, maimakon amfani da wadanda ke cikin masallatan.

Dama kafin hakan a makon da ya gabata an bude masallatai a wasu yankunan kasar da babu yawan masu cutar Korona, bayan shafe wattani uku a kulle.


/129